9 Yuni 2021 - 19:52
Kashi 95% Na Al'ummar Iran Na Amfana Da Iskar Gas Na Kasar

Ministan man fetur na kasar Iran Bijan Zangeneh ya bayyana cewa kashi 95% na mutanen kasar Iran su na amfani da iskar gas na dafa abinci a gidaje da wuraren ayyukansu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto ministan ya na fadar haka a safiyar yau a majalisar dokokin kasar, inda ya je don amsa tambayoyi dangane da ayyukan ma’aikatarsa.

Zangeneh ya kara da cewa matatun man kasar suna samar da ton 7,000 na samfurin CNG a kasar a ko wace shekara, sannan ana sarrafa ton 5,000 a cikin kasar sauran kuma Iran ta na saida sauran ga kasashen waje.

342/